ABNA24 : Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a lokacin da shugaban kasar Faransa ya tuntube shit a wayar tarho a daren jiya, inda suka tattauna kan halin da ake ciki dangane da batun shirin na Iran, da kuma yiwuwar gudanar da wani zama tare da bangaren Iran da kuma Amurka gami da kasashen turai.
Rauhani ya jaddada wa Macron cewa, Iran ta dauki matakai na jingine yin aiki da wasu daga cikin bangarorin yarjejeniyar ne sakamakon ficewar da Amurka ta yi, da kuma kasa cika alkawulla ga Iran daga bangaren kasashen turai.
Ya kuma sheda cewa, Iran din ba ta da wata matsala kan ci gaba da yin aiki da bangarorin da ta jingine yin aiki da su, matukar dai Amurka ta janye takunkuman da ta dora wa Iran, tare da yin aiki da yarjejeniyar daga dukkanin bangarorin da suka rattaba hannu a kanta.
Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya jaddada wajabcin yin aiki tare domin kubutar da wannan yarjejeniya daga rushewa, tare da kiran Iran da ta bayar da hadin kai domin ganin an cimma wannan manufa.
342/